Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Jami'an sojin ruwan Indonesia sun bayar da cikakkun bayanai game da kayan aikin soja da za a yi amfani da su wajen ayyukan agaji zuwa Gaza.
Jami'an sun bayyana cewa jiragen ruwa uku, wadanda ke aiki a karkashin kulawar rundunar sojin ruwan, sun sadaukar da kansu ne wajen kula da fararen hular Falasdinawa da suka jikkata a hare-haren Isra'ila a Gaza.
Your Comment